Rio 2016: An sake damke jami'in Kenya kan ruf da ciki

Asalin hoton, Getty Images
Kenya ta kare a mataki na 15 a jerin kasashen da suka fi samun lambar yabo a Rio 2016
An kama babban jami'in Kenya na biyar a binciken da ake yi kan bacewar kudi da kayayyakin wasanni bayan kammala gasar Olympic da aka yi a Rio a 2016.
Jami'an tsaron Kenya sun kama Ben Ekumbo, mataimakin shugaban kwamitin Olympic kuma shugaban wasan ninkaya na kasar a gidansa inda ya buya a karkashin gado.
Jami'an sun kuma sami akwatunan takalman gudu na kamfanin Nike da kayayyakin 'yan wasa da aka samar domin su yi amfani da su a wasannin guje-guje a gasar da aka kammala a Brazil.
An kama jami'in ne bayan da kwamitin bincike ya fitar da rahotansa cewar manyan jami'an da aka bai wa alhakin kula da wasannin sun sace sama da Fam miliyan 6 wadan da aka tanada domin kula da dawainiyar 'yan wasa.
A cikin watan Satumba ne aka kama wasu manyan jami'an harkokin wasannin Kenya, wadan da suka karyata dukkan zargin da ake yi musu.