Zakarun Turai: Ranieri na da kwarin guiwa

Claudio Ranieri,

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranieri ya ce burinmu mu yi nasara a wasan sannan mu koma Premier mu yi gyara

Kocin Leicester City Claudio Ranieri, na cike da fatan cewa kungiyarsa za ta kai zagayen 'yan 16 na gasar cin Kofin Zakarun Turai a wasan da za su yi da Club Brugge, Talatar nan.

Kocin dan Italiya ya nuna kwarin guiwarsa ne ganin cewa ko da canjaras suka tashi a wasan na yau Talata za su kai zagayen na biyu.

Zakarun na gasar Premier su ne na daya a rukuninsu na bakwai (Group G) bayan nasara uku da canjaras daya.

Kocin ya ce, ''muna da damar zuwa zagayen na gaba, ina mutunta Club Brugge sosai kuma ba na daukarsu cewa ba su da maki ko daya, suna wasa da kyau, wannan dai abin mamaki ne.''

Leicester ta ba da mamaki a fitowarta ta farko a gasar ta Zakarun Turai, duk da rashin kokarinta a Premier da ta yi ba zatta a bara.

Kungiyar ita ce ta 12 a teburin Premier bayan da ta yi rashin nasara karo na hudu a wasanninta bakwai, ranar Asabar a hannun Watford

Raneiri dan Italiya ya ce abin da za su ba fifiko shi ne su yi nasara a wasan na Talata, sannan su koma Premier su ga yadda za su gyara kansu

Dan wasansu mai tsada da suka sayo Islam Slimani, ba zai buga wasan ba saboda jiyyar raunin da ya ji a matse-matsinsa.

Shi ma dan wasansu na tsakiya Nampalys Mendy, yana jiyyar idon sawu, yayin da golansu Kasper Schmeichel ya ji rauni a hannu.