Za a kafa mutum-mutumin Ibrahimovic a Stockholm

Asalin hoton, others
Ibrahimovic ya yi wa Sweden wasa tsawon shekara 15, ashirin kuma a kungiyoyi
Za a kafa mutum-mutumin Zlatan Ibrahimovic a kofar filin wasan birnin Stockholm, bayan ya sake zama gwarzon dan wasan Sweden na shekara a karo na goma a jere.
A ranar Litinin ne aka ba wa dan wasan gaban na Man United, mai shekara 36 kwallon zinare ta wannan nasara('Guldbollen'), a wani biki da aka yi a babban birnin Sweden din, Stockholm.
Za a kafa mutum-mutumin nasa ne a kofar babban filin wasan (Friends Arena), inda ya ci Ingila kwallo hudu rigis a 2012, ciki har da wadda ya ci da baya daga nisan yadi 30.
Ibrahimovic ya ce: Wannan babban abu ne a wurina. Yawancin mutane sai sun mutu ake yi musu haka.''
A duk shekara tun 2007 yake samun lambar, kuma a 2005 ya samu, amma a 2006 dan wasan Arsenal Freddie Ljungberg ya kasa shi.
Ibrahimovic ya yi ritaya daga buga wa Sweden wasa bayan gasar kofin Turai ta 2016.
Ya ci wa kasar kwallo 62 a wasanni 116, kuma ya dauki kofin gasar lig-lig a kasashe daban-daban har hudu
games for Sweden and has won the domestic league title in four different countries.
Dan wasan da ya koma Man United a bara daga zakarun Faransa Paris St-Germain ya fito ne daga yankin Rosengard a gundumar Malmo ta Sweden din inda yawancin mazaunanta baki ne.