Steven Gerrad ya yi ritaya daga taka-leda

Gerrard ya yi ritaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gerrard ya ci wa Liverpool kwallaye 186

Tsohon dan wasan Ingila da Liverpool, Steven Gerrard, ya yi ritaya bayan shafe shekara 19 da ya yi yana taka-leda.

Gerrard mai shekara 36, ya buga wa Liverpool wasanni 710, inda ya lashe manyan kofuna takwas a kungiyar.

Daga baya ne ya koma kulob din LA Galaxy wanda ke buga gasar kwallon kafar Amurka a 2015.

Tsohon dan wasan tawagar Ingila, wanda ya yi mata wasanni 144 a matsayin dan kwallo na hudu da ya fi yawan taka-mata leda a tarihi, ya kuma jagorance ta a matsayin kyaftin a manyan gasa uku daga guda shida da ya fafata.

Gerrard ya fara wasansa na farko a Liverpool a watan Nuwambar 1998 a karawar da kungiyar ta yi da Blackburn Rovers, daga nan ne ya yi mata wasanni sama da 700.

Ana rade-radin cewa zai karbi aikin koci a kungiyar Celtic, ko kuma a bashi wani matsayi a Liverpool din.

Sai dai kawo yanzu ba a bayyana takamaiman abin da tsohon dan kwallon zai yi ba.