Kotu ta nemi a daure Neymar shekara 2

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Neymar da babansa da tsohon shugaban Barcelona, Rosell za su gurfana a kotun

Masu gabatar da kara na Spaniya sun nemi da a daure dan wasan gaba na Barcelon Neymar shekara biyu a kurkuku, kan rawar da ya taka a rashawar cinikinsa daga kungiyar Santos ta Brazil a 2013.

Alkalin kotun Jose Perals, ya kuma nemi da a tura tsohon shugaban Barcelona Sandro Rosell gidan maza tsawon shekara biyar, kuma a ci tarar kungiyar ta Spaniya euro miliyan 8.4 (fan miliyan 7.2).

Kotun ta kuma nemi a yi watsi da tuhumar da ake yi wa sabon shugaban Barcelonan Josep Maria Bartomeu.

Karar dai ta samo asali ne daga korafin da wani kamfanin Brazil (DIS) ya yi, wanda yake da kashi 40 cikin dari na kason cinikin dan wasan.

kuma ya yi korafin cewa ba a ba shi yawan kudin da ya kamata a ba shi ba.

Barcelona ta yi tsammanin ta kawo karshen karar, lokacin da wani alkali Jose de la Mata, a watan Yuni ya ayyana sasantawa tsakanin masu gabatar da kara da kungiyar.

A sasanton Barcelonan ta biya tarar fan miliyan 4.7, ta kaucewa tuhumar kin biyan haraji.

Sai dai kuma babban mai gabatar da kara na kasar ya daukaka kara a kai aka yi watsi da wancan hukunci na dakatar da karar a watan Satumba, inda aka bayar da damar ci gaba da shari'ar.

A farkon shekarar nan aka yanke wa abokin wasan Neymar din a Barcelona, Messi hukuncin zaman gidan yari na wata 21 bisa laifin kaucewa biyan haraji.

Messin ya daukaka kara, kuma bisa dokokin kasar wa'adin zaman yari da bai kai shekara biyu ba, ana idage shi, sai mutum ya sake laifi a aiwatar da hukuncin.

Tun lokacin da ya koma Nou Camp, Neymar mai shjekara 24 ya dauki kofin La Liga 2 da Copa del Rey 2, da kofin Zakarun Turai.

Sauran kofunan da ya dauka su ne kofin manyan Zakarun Turai, da kofin zakarun Spaniya da kuma kofin duniya na kungiyoyi.

A watan Oktoba ya sake kulla yarjejeniyar zaman shekara biyar a Barcelonan.