Man United za ta sabunta kwantiragin Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A bana Ibrahimovic ya ci wa United kwallo 17 a wasanni daban-daban.

Kungiyar Manchester United za ta tsawaita kwantiragin shekara daya na Zlatan Ibrahimovic da wata shekara dayar.

A lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasan da ta gabata ne tsohon dan wasan na Sweden ya koma United bayan wa'adin zamansa a PSG ya kare.

Dan wasan mai shekara 35 ya kulla yarjejeniyar komawa Manchester United din ne da sharadin kara wa'adin zaman nasa da wata shekara daya.

Jose Mourinho ya ce, '' za mu aiwatar da tanadin kwantiragin nasa na karin shekara daya, bayan nan kuma zai iya yin abin da ya ga dama.