Tsohon dan wasan Ingila, Stewart ya fasa kwai

Paul Stewart

Asalin hoton, ALLSPORT

Bayanan hoto,

Stewart wanda ya yi Tottenham da Liverpool da Manchester City, ya fadi yadda wani koci ya rika lalata da shi har shekara 4

Tsohon dan wasan Ingila da Tottenham Paul Stewart ya bayyana cewa an ci zarafinsa ta lalata da shi lokacin yana matashin dan wasa.

Stewart, wanda ya fara wasa a matsayin kwararre da Blackpool ya kuma yi wa Man City da Liverpool wasa, ya sheda wa jaridar Mirror yadda wani koci da bai fadi sunansa ba ya rika lalata da shi kullum tsawon shekara hudu.

Dan wasan ya fasa kwan ne, bayan da wasu tsoffin 'yan wasan kungiyar Crewe su ka bayyana cewa wani kocinsu ya rika lalata da su lokacin suna yara.

Mutane 11 ne suka gana da ofishin 'yan sanda na Cheshire, tun lokacin da daya daga cikin tsoffin 'yan wasan, Andy Woodward, ya fito fili ya fasa kwai kan lamarin.

Asalin hoton, ANDY WOODWARD

Bayanan hoto,

Tsohon dan wasan Crewe da Sheffield United da Bury Andy Woodward na daga wadanda suka fasa kwai

Woodward da Steve Walters sun bayyana yadda kocinsu a lokacin Barry Bennell, wanda aka daure shekara tara a 1998 ya rika lalata da su.

Shugaban kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta Ingila Gordon Taylor ya ce yana tsammanin wasu karin 'yan wasan da aka yi lalatar da su, su fito fili su fada.

Shi dai Stewart ya gaya wa jaridar ta Mirror cewa kocin ya rika lalata da shi har ya lokacin da ya kai shekara 15, kuma kocin ya yi masa barazana cewa zai kashe danginsa idan har ya sake ya fada.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

An daure koci Barry Bennell shekara tara a 1998 saboda luwadi da matasan 'yan wasansa