An yi satar shiga Old Trafford

Uosof Ahmadi

Asalin hoton, UOSOFAHMADI

Bayanan hoto,

Uosof Ahmadi a hannun hagu ya taba jarraba hakan a filin wasan Arsenal a watan Nuwamba

Wasu magoya bayan Man United biyu da suka boye a bandakin Old Trafford suka kwana a daren Juma'a domin su kalli wasan kungiyar da Arsenal kyauta sun fitar da bidiyon yadda suka tsara abin.

Magoya bayan suna cikin tawagar da ta je ziyarar bude ido a filin wasan ne, amma suka sulale daga cikin abokan ziyarar tasu, suka buya, domin kallon wasan.

A ranar Asabar da safe ne aka gano su, a lokacin da ake bincike filin wasan, domin shirye-shiryen wasan.

Daya daga cikin matasan biyu mai suna Uosof Ahmadi ya gaya wa BBC cewa su kam sun yi tsammanin komai zai tafi daidai saboda irin dabarar da suka yi suka tsara abin.

Matashin dan shekara 21, ya ce, shirin na kwanan zaune na sa'a 24, abu ne da ake yi a YouTUbe, kuma yadda ya shafe dare a shagon M&M World da gidan abinci na McDonald, ya sanya hoton bidiyonsa na yadda ya yi kokarin gwada irin wannan abu a filin wasan Arsenal a farkon watan nan.

Bayan da masu kula da filin sun kama Uosof Ahmadi da abokinsa Kyle Morgan-Williams sun mika su ga 'yan sanda, wadanda su kuma suka sallame su ba tuhuma.

Asalin hoton, Uosof Ahmadi

Bayanan hoto,

Matasan biyu sun shafe dare ne a bandaki

Lamarin ya faru ne watanni shida bayan da kwatsam aka dage wasan Premier na Man United da Bournemouth a filin, lokacin da aka gano kunshin wani abu a filin.

Daga baya an gano cewa wani abin fashewa ne na bogi da ka bari a filin bayan atisayen 'yan wasa a makon.