White: Ni ma kocinmu ya yi lalata da ni

David White

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

David White ya rubuta littafi a kan yadda luwadin da kocin ya yi masa ya sauya rayuwarsa

Tsohon dan wasan Man City da Ingila David White, ya zama na hudu cikin tsoffin 'yan wasan da ke fitowa su fadi yadda koci-kocinsu suka rika lalata da su, lokacin suna matasan 'yan wasa.

White ya biyo bayan tsoffin 'yan wasan kungiyar Crewe Andy Wodward da Steve Walters da kuma tsohon dan wasan Tottenham Paul Steward, da suka fasa kwan kan wannan badala.

Tsohon dan wasan mai shekara 49, shi ma ya ce tsohon kocin Crewe Barry Bennell, wanda aka daure bisa laifin lalata da yara, ya yi masa luwadi.

A wata sanarwa da ya fitar, White ya ce Bennell ya yi lalata da shi a karshen shekarun 1970 da kuma farko-farkon 1980, lokacin yana wasa a kungiyar matasa ta Whitehill a Manchester.

Ya ce bisa wasu dalilai da dama, kuma tsawon kusan shekara 20, ya yi gum da bakinsa kan wannan abin bakin ciki, bai gaya wa iyayensa ba ko abokansa.

Ya ce, a shekarar da ta wuce ya yanke shawarar rubuta littafi kan rayuwarsa, amma bai so ya ambaci wannan badala da aka yi masa ba yana matashi, amma ya ga ba mafita sai ya yi.

Kuma wurin yin hakan, ya ga lalle dole ne ya yarda cewa abin da Bennell ya yi masa ya yi tasiri a kusan duk wani abu na rayuwarsa