Arsenal ta yi wasanni 18 a jere ba a doke ta ba

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arsenal tana mataki na hudu a kan teburin Premier

Arsenal ta fafata a wasanni 18 a jere ba tare da an doke ta ba tun lokacin da aka fara gasar wasannin bana.

Arsenal wadda ta fara buga gasar Premier ta bana da Liverpool a ranar 14 ga watan Agusta ta sha kashi a Emirates da ci 4-3, tun daga lokacin ne ta yi wasanni daban-daban sau 18 ba a doke ta ba.

Gunners wadda ta fafata a gasar cin kofin Premier da na zakarun Turai da League Cup ta ci wasanni 12 ta kuma yi canjaras sau shida.

Haka kuma tun fara kakar bana, Arsenal ta zazzaga kwallaye 46 a raga, inda aka zura mata 17 a tata ragar.

Wasan da Arsenal ta ci kwallaye da yawa tun fara kakar bana shi ne wanda ta doke Ludogorets da ci 6-0 a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 19 ga watan Oktoba.

Arsenal ce ta yi ta biyu a rukunin farko a gasar cin kofin zakarun Turai da maki 11, yayin da kungiyar ke mataki na hudu a teburin gasar Premier da maki 25.