Kwallon kafar mata: Kamaru za ta kara da Zimbabwe

Asalin hoton, Getty Images
Kamaru ta kai wasan zagaye na biyu a gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirka ta mata
Mai masaukin baki Kamaru za ta fafata da Zimbabwe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon kafar mata a wasa na uku na cikin rukuni a ranar Juma'a.
Kamaru wadda ta yi wasanni biyu a rukunin farko ta ci wasanni biyu, inda ta samu nasarar doke Masar 2-0 a wasan farko sannan ta ci Afirka ta Kudu daya mai ban haushi.
Ita kuwa Zimbabwe maki daya ne kadai take da shi, bayan da ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Afirka ta Kudu a wasan farko na cikin rukuni, a wasa na biyu kuwa Masar ce ta doke ta da ci daya mai ban haushi.
Haka kuma a ranar ta Juma'a za a kece raini tsakanin Masar da Afirka ta Kudu.
Kamaru ce ta daya a rukunin farko da maki shida sai Masar ta biyu da maki uku, yayin da Afirka ta Kudu da Zimbabwe kowacce ke da maki dai-dai.