Watakila Mikel Obi ya bar Chelsea a Janairu

Watakila Mikel ya bar Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mikel Obi ya koma Chelsea a shekarar 2006

John Mikel Obi ya bayar da hasken cewar watakila zai iya barin kungiyar Chelsea a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafar Turai.

Mikel wanda ya yi shekara 10 a Chelsea, bai buga wasa ko daya ba a kakar bana, duk da cewar shi ne dan kwallon kungiyar na biyu da ya fi dadewa a Stamford Bridge, bayan kyaftin John Terry.

Dan wasan wanda ya koma Chelsea a 2006 kan kudi fam miliyan 16, ya lashe kofunan Premier biyu da na FA hudu da na kofin zakarun Turai dana Europa.

Sai dai kuma tun lokacin da kungiyar ta nada Antonio Conte a matsayin sabon kociyanta a bana, bai saka Mikel Obi a wasannin da ya jagoranta ba.

Kociyan Nigeria, Gernot Rohr, ya ce Chelsea ta yi watsi da Mikel ne, saboda ya wakilci Nigeria a gasar Olympic da aka yi a Brazil.