Kompany zai yi jinyar sati shida

Kompany zai yi jinyar sati shida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 27

Mai horar da Manchester City, Pep Guardiola, ya ce kyaftin din kungiyar Vincent Kompany zai yi jinya sati shida, sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.

Komapany dan kwallon tawagar Belgium ya yi rauni ne a karawar da City ta ci Crystal Palace 2-1 a wasan Premier da suka yi a ranar Asabar.

Dan kwallon na fama da yin jinya tun fara kakar wasan bana, kuma wasanni biyu kacal ya buga wa City a fafatawar da ta yi.

Wannan kuma shi ne karo na 35 da Komapany ke yin rauni a wurare dabam-dabam tun komawarsa City daga Hamburg a shekarar 2008.