Hira da aka yi da Mikel kan dalilin da baya buga wa Chelsea wasanni a bana

Hira da aka yi da Mikel kan dalilin da baya buga wa Chelsea wasanni a bana

John Mikel Obi ya bayar da hasken cewar zai iya barin kungiyar Chelsea a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafar Turai.

Mikel wanda ya yi shekara 10 a Chelsea, bai buga wasa ko daya ba a kakar bana, duk da cewar shi ne dan kwallon kungiyar na biyu da ya fi dadewa a Stamford Bridge, bayan kyaftin John Terry.

Dan wasan wanda ya koma Chelsea a 2006 kan kudi fam miliyan 16, ya lashe kofunan Premier biyu da na FA hudu da na kofin zakarun Turai dana Europa.