Kwallon kafar mata: Kamaru ta kai wasan daf da karshe

Gasar kwallon kafar Afirka ta mata

Asalin hoton, Super Sports

Bayanan hoto,

Kamaru ta kai wasan daf da karshe a gasar kwallon kafar mata ta Afirka

Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta kai wasan daf da karshe a gasar kwallon kafa ta mata ta cin kofin nahiyar Afirka, bayan da ta ci ta Zimbabwe 2-0 a karawar da suka yi a ranar Juma'a.

Da wannan sakamakon Kamaru ta hada maki tara ta kuma jagoranci rukunin farko, bayan da ta ci Masar 2-0 ta kuma doke Afirka ta Kudu daya mai ban haushi.

A wasa na biyu na rukunin farko, ita ma Afirka ta Kudu ta kai wasan daf da karshe, bayan da ta casa Masar da ci 5-0.

Afirka ta Kudu ta hada maki hudu, bayan da ta yi canjaras babu ci da Zimbabwe, ta kuma sha kashi a hannun Kamaru da ci daya mai ban haushi.

Sai a ranar Asabar rukuni na biyu zai karasa wasanninsa na uku, inda za a kece raini tsakanin Mali da Ghana da kuma kece raini tsakanin Kenya da Nigeria.