Ingila: Dambe ya ci matashi

Asalin hoton, MAGDALENA MOCZYK
Kuba Moczyk ya fadi ne bayan da abokin dambensa ya naushe shi a ka
Wani matashin dan damben boksin ya mutu sakamakon raunin da abokin karawarsa ya yi masa a ka a dambensa na farko
An doke Kuba Moczyk, mai shekara 22 ne a turmi na uku ranar Asabar a filin wasa na Tower Complex a garin Great Yarmouth na Ingila.
Iyalansa sun ce ya mutu ne ranar Laraba da dare a asibitin James Paget a Gorleston, inda yake kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Kakakin asibitin ya ce iyalan Mista Moczyk na kusa da shi lokacin ya cika, kuma an bayar da wasu daga cikin sassan jikinsa taimako domin yin amfani da su wajen dashe ga marassa lafiyar da ke bukata.
Kocin dan damben, Scott Osinski ya ce, Mr Moczyk na kan yin nasara a damben kafin abokin karawar tasa, dan sheakara 17, ya yi masa wannan naushin da ya kwantar da shi.
Tsohon kocinsa kuma mai hada dambe a yanzu Leon Docwra, ya ce daga yanzu ya hana 'ya'yansa dan shekara 11 da kuma 16 damben boksin.
Hukumar garin na Great Yarmouth Borough, ta ce wurin da aka yi damben yana da lasisin daukar wasan dambe, amma jami'an kula da lafiyar muhalli za su gudanar da bincike, saboda an yi korafi kan irin matakan kula da lafiya na wurin.