An bukaci a daure Eto'o shekara 10

Samuel Eto'o

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Samuel Eto'o ya musanta duk wani zargi na kin biyan haraji

Masu gabatar da kara a Spaniya sun nemi kotu ta daure tsohon dan wasan Barcelona da kamaru Samuel Eto'o, sama da shekara 10 kan kin biyan haraji.

Suna zarginsa ne da kafa kamfanoni da yawa domin ya kauce wa biyan haraji lokacin da yake Barcelona, daga 2004 zuwa 2009.

Bayan hukuncin daurin shekara goma da wata shida masu gabatar da karar suna kuma son kotu ta ci tsohon dan wasan na Barcelona

tarar dala miliyan 15 da dubu 100 bisa laifuka hudu da suke zarginsa na kin biyan harajin dala miliyan hudu a shekarun da ya yi a kungiyar

Masu gabatar da karar suna kuma neman a yanke wa wakilin dan wasan a lokacin da yake kungiyar Jose Maria Mesalles irin wannan hukunci.

Ba a dai samu jin ta bakin Eto'o da lauyoyinsa ba kan zargin, amma tun a baya dan wasan ya taba musanta yin wani abu ba daidai ba game da biyan harajin.

Eto'o na daga cikin 'yan wasan Barcelona na da da na yanzu da suke fuskantar shari'a a Spain.

is among other current and past Barcelona players facing legal problems in Spain.

A watan Yuli, an yanke wa Lionel Messi da mahaifinsa hukuncin zaman gidan yari na wata 21 bisa laifin kin biyan haraji.

Sai dai ba a tura su gidan mazan ba, saboda bisa dokokin Spain idan wa'adin yari bai kai shekara biyu ba a masu laifi karon farko za a iya dage shi.

A yanzu Neymar da mahaifinsa da Barcelona ma na fuskantar shari'a daga hukumomin Spain kan zargin almundahana a cinikin dan wasan na Brazil daga Santos a 20134.