Kofin Afirka: Kenya ta koka da kanta

A wasa na gaba za a samu sauran kungiyoyin da za su kai wasan kusa da karshe
Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Kenya Doreen Nabwire ta ce su ke da alhakin rashin tabuka komai da suka yi a gasar kofin Afirka da ake yi a Kamaru.
Kocin ta ce: ''Dukkaninmu ba mu ji dadin abin da ya faru ba ko kadan, saboda mun yi shiri sosai tun lokacin da muka samu damar zuwa gasar.
Saboda haka, sai dai kawai mu dora wa kanmu alhakin hakan, amma zamu kori gaba''
Daga cikin wasannin da suka yi 'yan Harambee Starlets din a rukuninsu na biyu (Group B) ba su ci wasa ko da daya ba.
Mali ta ci su uku da daya, yayin da Ghana ta ci su uku da daya ita ma, sannan kuma za su yi wasansu na uku da Najeriya ranar Asabar.
A wannan rukuni nasu na biyu Mali za ta hadu da Ghana, su ma a ranar Asabar din
Kasancewar Kenya ba ta ci wasa ko da daya ba yanzu sun yi waje a gasar, duk da wasan da za su yi da Najeriya ta daya a rukunin, wanda Ghana ke bi mata baya.
A wasan rukuni na daya (GroupA), mai masauki baki Kamaru za ta hadu da Zimbabwe, yayin da Masar za ta fafata da Afirka ta Kudu a ranar Juma'a.