Europa: Man U ta doke Feyenoord 4-0

Wayne Rooney scoring

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saura kwallo daya Rooney ya kamo Sir Bobby Charlton wajen ci wa Man United yawan kwallaye

Manchester United ta kara damarta ta zuwa zagaye na gaba na 'yan 32 a gasar kofin Zakarun Turai na Europa, bayan ta doke Feyenoord 4-0.

Rooney ne ya fara cin kwallo minti 35 da shiga filin na Old Trafford, bayan an dao daga hutun rabin lokaci a minti na 69 kuma sai Mata ya kara.

Mai tsaron ragar bakin Jones, ya ci kansu da wata kwallo da Ibrahimovic ya yi kokarin bayar wa, ta bi ta tsakankanin kafarsa ta fada raga.

Lingard ne ya ci wa Man United kwallo ta hudu bayan an shiga karin lokaci na tashi.

Nasarar ta sa kungiyar ta Premier ta zama ta biyu a rukuninsu na daya (Group A), da maki tara a wasanni biyar.

Fenerbahce tana matsayin ta daya da maki 10 bayan da ta doke Zorya 2-0.

Yanzu Manchester United na bukatar ko da canjaras a wasanta na karshe a gidan Zorya ranar Alhamis 8 ga Disamba, ta kai zagaye na gaba.

Southampton:

Ita kuwa Southampton ta kara shiga tsaka-mai-wuya, bayan da Sparta Prague da ta karbi bakuncinta ta ci ta 1-0.

Yanzu Southampton din na bukatar canjaras ba ci akalla, a karawar da za ta yi da Hapoel Be'er Sheva a wasansu na karshe kafin ta kai zagaye na gaba na gasar ta Europa.

Za ta yi wasan ne ranar takwas ga watan Disamba a gidanta