Real Madrid ta doke Sporting Gijon 2-1

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye 10 a kakar bana

Real Madrid ta ci Sporting Gijon 2-1 a gasar cin kofin La Liga wasan mako na 13 da suka kara a ranar Asabar.

Tun a minti na 18 da fara wasan Real Madrid ta ci kwallayenta biyu ta hannun Cristiano Ronaldo.

Kwallon farko ya ci ne da fenariti, sannan ya ci ta biyu da ka, hakan ya sa yana da kwallaye 10 da ya ci jumulla tun fara kakar bana.

Sporting Gijon ta farke kwallo daya ta hannu Carlos Carmona, kuma saura minti 13 a tashi daga karawar Duje Cop ya barar mata da fenariti.

Real Madrid ta ci gaba da zama a kan teburin La Liga da maki 33, ita kuwa Sporting Gijon tana da maki tara a mataki na 18.