Chelsea ta ci gaba da zama a kan teburin Premier

EPL

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Chelsea ta ci wasanni bakwai a jere

Kungiyar Chelsea ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier, bayan da ta ci Tottenham 2-1 a wasan mako na 13 da suka yi a ranar Asabar.

Tottenham ce ta fara cin Chelsea kwallo ta hannun Christian Eriksen tun a minti na 11 da fara tamaula.

Sai dai kuma daf da za a je hutu Pedro ya farke kwallon.

Victor Moses ne ya ci wa Chelsea kwallo na biyu, wanda hakan ya bai wa kungiyar damar hada maki uku a fafatawar.

Chelsea tana kan teburin Premier da maki 31, sai Liverpool ta biyu da maki 30, yayain da Manchester City ke matsayi na ita ma da maki 30.