Bahagon Sisco da Abban Na Bacirawa sun yi canjaras

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Wasanni shida aka taka a gidan damben Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria

Manyan wasanni shida aka dambata a gidan damben gargajiya na Ali Zuma da ke Dei-Dei Abuja, Nigeria a ranar Lahadi.

Ciki har da wasan da aka yi turmi uku babu kisa tsakanin Bahagon Sisco daga Kudu da Abban Na Bacirawa daga Arewa.

Tun farko sarkin mawakan 'yan damben gargajiya Autan Mai Turare ne ya hada su wasan, bayan da ya wasa Bahagon Sico sannan ya yi wa Bahagon Abba kirari.

An fara bude fili ne da karawa tsakanin Shagon Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Shagon Dogon Minista daga Kudu, kuma turmi uku suka yi babu kisa.

Nan da nan aka sa zare a damben da Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya doke Garkuwan Mahorata daga Arewa.

Damben Shagon Dan Matawalle daga Kudu da Shagon Bahagon Musa daga Arewa an kare ne da takaddama, bayan da aka buge Shagon Dan Matawalle a wajen filin wasa.

Karawar da ka yi tsakanin Shagon Shagon 'Yar Tasa daga Arewa da Shagon Bahagon Dan Kanawa babu kisa a turmi ukun da suka dambata.

Wasa ma tsakanin Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu da Garkuwan Mahorata daga Arewa babu wanda ya je kasa a turmi ukun da suka yi.