Ribery ya tsawaita zamansa a Munich

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ribery ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta Turai a 2013

Tsohon dan kwallon tawagar Faransa, Franck Ribery, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Bayern Munich zuwa Junin 2018.

Ribery mai shekara 33, wanda ya ci wa Munich kwallaye 108 a wasanni 333 da ya buga, ya yi shekara goma yana murza-leda a kungiyar da ke buga gasar Jamus.

Dan wasan ya lashe kofunan gasar Bundesliga shida tun komawarsa can daga Marseille a shekarar 2013, ya kuma ci kofin zakarun Turai, wanda kungiyar ta dauka a 2013.

Ribery ya buga wa Munich wasanni 12, inda ya kuma ci kwallaye biyu a kakar bana.