Kwallon kafar mata: Kamaru da Ghana

Women Soccer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamaru ba ta taba lashe kofin nahiyar Afirka a kwallon kafar mata ba

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Kamaru za ta kara da ta Ghana a wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata a ranar Talata.

Kamaru mai masaukin baki ta kai wannan matakin ne, bayan da ta jagoranci rukunin farko da maki tara, yayin da Ghana ta yi ta biyu da maki bakwai a rukuni na biyu.

Haka kuma za a kece raini a wasan hamayya tsakanin Nigeria da Afirka ta Kudu a daya wasan daf da karshe a dai ranar ta Talata.

Nigeria wadda ke rike da kofin Afirka ta kai wasan daf da karshe ne, bayan da ta yi ta daya a rukuni na biyu da maki bakwai, inda Afirka ta Kudu ce ta yi ta biyu a rukunin farko da maki hudu.

Wannan ce gasar nahiyar Afirka ta mata ta 12 da ake fafatawa, inda Super Falcons ta lashe kofin sau tara, yayin da Equatorial Guinea ta ci guda biyu.