Arsenal ta doke Bournemouth 3-1

EPL

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Arsenal ta ci gaba da zama a matsayi na hudu a kan teburin Premier da maki 28

Arsenal ta ci Bournemouth 3-1 a gasar Premier wasan mako na 13 da suka kara a Emirates a ranar Lahadi.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Alexis Sanchez a minti na 12 da take leda, bayan da Steve Cook na Bournemouth ya yi kuskuren mayar da kwallo gida.

Bournemouth ta farke kwallo a bugun fenariti ta hannun Callum Wilson, bayan da mai tsaron bayan Arsenal, Nacho Monreal ya yi masa keta a da'ira ta 18.

Bayan da aka dawo daga Hutu ne Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo na biyu, sannan Sanchez ya ci ta uku kuma ta biyu da ya zura a ragar Bournemouth a wasan.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 28, bayan da Chelsea ke kan teburin da maki 31, sai Liverpool da City masu maki 30 kowaccensu.