Rosberg ya lashe tseren Formula 1 na bana

Asalin hoton, Getty Images
Rosberg dan kasar Jamus shi ne ya lashe tseren motoci na bana
Nico Rosberg ya lashe tserensa na motocin Formula 1 na farko na duniya, duk da kin bin umarnin tawagar Marsandi da Hamilton ya yi, bayan da ta bukaci direban da ka da ya dauki tseren a matsayin na Hamayya.
Hamilton ne ya lashe atisayen fitar da jerin wadanda za su zama a sawun gaba-gaba a gasar ta Abu Dhabi, duk da cewar sai Rosberg ya yi na uku ne Hamilton zai zama zakaran bana.
Rosberg matukin Marsandi ya fuskanci kalubale a wajen Sebastian Vettel matukin Ferrari, amma duk da haka ya lashe gasar bana da maki 385.
Haka kuma Hamilton ne ya yi na biyu a bana da maki 380, yayin da Vettel ya kammala tseren Abu Dhabi a mataki na biyu.