Man United da West Ham sun buga 1-1

Asalin hoton, Getty Images
United ta ci gaba da zama a matsayi na shida a kan teburin Premier
Manchester United da West Ham sun tashi kunnen doki 1-1 a gasar Premier wasan mako na 13 da suka kara a Old Trafford a ranar Lahadi.
West Ham United ce ta fara cin kwallo ta hannun Diafra Sakho dakika biyu da fara wasa.
Sai a minti na 21 ne United ta farke kwallon ta hannun Zlatan Ibrahimovic.
An kuma kori Jose Mourinho kociyan United daga wasan, bayan da ya yi bal da robar ruwan sha, a lokacin da aka bai wa Paul Pogba katin gargadi bisa faduwa kasa da gangan.
Wannan ne karo na biyu da aka kori kociyan na Manchester United bayan ta farko da aka yi masa a gasar Premier da suka tashi babu ci da Burnley a watan jiya.
United tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 20, yayin da West Ham ke matsayi na 16 da maki 12.
Manchester United za ta sake karbar bakuncin West Ham a League Cup a ranar Laraba 30 ga watan Nuwamba.