'Ana nuna wa bakake bambanci a Snooker'

Asalin hoton, Getty Images
Karbar Musulunci da na yi shi ne babban abin jin dadi gareni
Kwararren dan wasan kwallon tebur ta snooker guda daya tilo a duniya ya ce hukumar kwallon zunguren ta duniya ba ta yin wani abu na karfafa wa bakaken fata guiwa su shiga wasan.
Tun a lokacin da ya shiga cikin jerin kwararrun wasan na duniya a 2001, Rory McLeod, wanda ke Leicester a Ingila, shi ne har yanzu bakar fata daya da yake shiga gasar wasan.
McLeod mai shekara 45, ya zargi hukumar wasan na snooker da cewa ita ba abin da ya dame ta sai kudin da ake ci a wasan da kuma kamfanonin da ke daukar nauyin gasar wasan.
Dan wasan wanda ya musulunta a 2004, a lokacin ya bayyana cewa wannan mataki da ya dauka na karbar Musulunci na daya daga cikin shawara mafi kyau da ya yanke a rayuwarsa.
Bayan Hamza Akbar na Pakistan da Hossein Vafaei Ayouri na Iran da Hammad Miah na Hertford da Hatem Yassen na Masar, yana daga cikin 'yan wasan biyar Musulmi, wadanda ke cikin jerin kwararrun wasan na Snooker na duniya.
Asalin hoton, Rex Features
Da za a karfafa wa bakaken fata guiwa, da yawa da sun shigo wasan
Dan wasan wanda ya samu gagarumar nasara a shekarar da ta wuce a gasar da aka yi ta Ruhr a Jamus ya ce abu ne mai wuya wasu bakaken fata su samu cigaba a wasan kamarsa, saboda rashin daukar nauyinsu ko samar musu da kudade.
McLeod wanda dan asalin kasar Jamaica ne, ya ce akwai bukatar a samu bakaken fata a kungiyoyin kwallon snooker.
Sai dai kuma shugaban hukumar wasan na snooker ta duniya Jason Ferguson ya kare zargin da cewa, suna ba wa kowa dama a wasan, ba wani bambnci a suke nunawa, idan ka kware a wasan za ka shiga jerin gwanayen.