Luwadi: An garzaya da koci asibiti

Barry Bennell

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Tsoffin 'yan wasa da dama sun ce Bennell ya yi luwadi da su, lokacin suna matasan 'yan wasa karkashinsa

An garzaya asibiti da tsohon kocin matasa na kwallon kafa Barry Bennell, wanda 'yan wasa da dama a Ingila ke ta fitowa suna bayyana cewa ya yi luwadi da su, lokacin suna matasa, bayan an same shi a sume.

'yan sandan Thames Valley a Ingila sun ce, bayan da suka samu kiran kai dauki na gaggawa ne, suka sami kocin mai shekara 62 a wannan hali, inda suka garzaya da shi asibiti.

Shi dai Bennell din an daure shi shekara hudu bisa laifin yi wa wani yaro dan Birtaniya fyade, lokacin da suka je wani yawon wasannin kwallon kafa a Florida a 1994.

Kuma an yi masa hukuncin daurin shekara tara a 1998 a kan laifukan lalata da wasu yara maza su shida a Ingila.

Mako biyu da ya wuce, tsohon dan wasan kungiyar matasa ta kwallon kafa ta Crewe, Andy Woodward ya fito fili ya bayyana irin yadda koci Bennell ya rika lalata da shi tsawon shekaru, lokacin yana matashi.

Tun daga wannan lokacin ne kuma 'yan wasa da dama suka fito suke bayyana yadda su ma tsohon kocin ya rika luwadi da su.

A yanzu hukumomi daban-daban na gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake ta yi a kan tsohon kocin.