Tony Pulis ya sha kaye a kotu

Tony Pulis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kotu ta ci tararsa ne kan karya alkawarinsa da Crystal Palace

Kocin West Bromwich Albion Tony Pulis ya yi rashin nasara a karar da ya daukaka kan cin tararsa fan miliyan 3.7 da zai biya tsohuwar kungiyarsa Crystal Palace.

A farkon wannan shekarar ne kotun sauraren kararrakin wasan Premier ta yanke hukuncin cewa Pulis ya biya Crystal Palace kudin a matsayin tara kan yadda ya bar kungiyar a rigimar da suke yi a farkon kakar 2014-15.

Crystal Palace ta kai karar kocin a lokacin da zargin cewa ya yaudare ta, har ta biya shi fan miliyan biyu a matsayin kudin wata garabasa, zargin da ya musanta

A kan haka ne kocin ya daukaka kara, wadda kuma bai yi nasara ba.

Shi dai Pulis yana da kwantiragi ne da kungiyar ta kudancin Landan, wadda ta yi alkawarin ba shi fan miliyan biyu rara, idan ba su fadi daga Premier ba a karshen kakar 2013-14.

Sannan kuma zai ci gaba da zama a matsayin kocinta har zuwa 31 ga watan Agusta na 2014.

Kocin ya cika alakawarinsa na ganin kungiyar ba ta fadi daga Premier ba, amma kuma bai tsaya ba har zuwa ranar da aka yi yarjejeniya zai iya barinta, sai ya nemi a ba shi rarar kudin da aka yi masa alkawari.

Kuma bayan kwana daya ya ce zai tafi daga kungiyar ta Crystal Palace, inda ya bar ta ranar 14 ga watan Agusta, ranar jajiberin sabuwar kaka.