Sunayen gasar gwarzon dan wasan BBC na Burtaniya

BBC Sports Personality of the Year 2016

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Wadanda za a zabi gwarzon shekarar a cikinsu ranar 18 ga watan Disamba

An fitar da sunayen 'yan wasa daban-daban domin zaben gwarzon dan wasan Burtaniya na BBC na 2016.

A ranar Lahadi 18 ga watan Disamba ne a Birmingham, jama'a za su zabi gwaninsu ta waya ko ta intanet yayin shirin da za a nuna kai tsaye. Wadanda aka zaba su ne:

Nicola Adams - damben boksin, da Gareth Bale - Kwallon kafaFootball da Alistair Brownlee - wasan linkaya da tseren keke da gudun famfalaki, da Sophie Christiansen - Sukuwar dawaki, da Kadeena Cox - guje-guje da tsalle-tsalle, da Mo Farah - Gudun yada kanin wani, da Jason Kenny - Tseren keke, da Laura Kenny - Tseren keke.

Andy Murray - Kwallon Tennis Tennis, da Adam Peaty - Linkaya, da Kate Richardson-Walsh - Kwallon gora, da Nick Skelton - Sukuwar dawaki, Dame Sarah Storey - Tseren keke, da Jamie Vardy - Kwallon kafa, da Max Whitlock - Wasan alkafura, da Danny Willett - Kwallon Golf.

An zabo sunayen 'yn wasan 16 ne na bana bayan nasarorin da Burtaniya ta yi a wasanni dabn-daban da suka hada d gasar Olympics da Olympics din nakasassu a Rio.