An tuhumi Mourinho da rashin da'a

Jose Mouriho kicking water bottle

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mourinho lokacin da ya yi bal da robar ruwa saboda alkalin wasa ya ba wa Pogba kati

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi kocin Man United Jose Mourinho saboda bal da ya yi da robar ruwa kan fusata da ya yi a wasan da suka yi 1-1 da West Ham a Old Trafford ranar Lahadi.

A ranar Litinin aka tuhumi Mourinho, mai shekara 53, wanda alkalin wasa Jon Moss, ya kore shi zuwa cikin 'yan kallo a kan bene, da rashin da'a.

Yana da damar mayar da martani da bayar da bahasinsa a kan tuhumar, daga yanzu zuwa karfe shida na yamma agogon GMT ranar daya ga watan Disamba.

Wannan shi ne karo na biyu da ake tuhumar kocin dan Portugal a cikin wata biyu, domin alkalin was ya kore shi a lokacin wasansu da Burnley ranar 29 ga watan Oktoba.

A kan hakan aka haramta ma sa halartar wasa daya da kuma cin tararsa fan 8000.

Saboda tuni an taba korarsa daga fili a bana, yanzu wata hukuma ce daban za ta yi hukuncin laifin da ya yi ranar Lahadi, wanda ba asan zai amince ya aikata ba ko zai ki yarda ya yi.

Dama a baya ma an taba cin tarar tsohon kocin na Chelsea da Inter da Real Madrid fan dubu 50 game da kalaman da ya yi.

A wasan na ranar Lahadi Mourinho ya fusata ne bayan da alkalin wasa ya ba wa Paul Pogba katin gargdi saboda faduwa da ya yi kamar kyaftin din West Ham Mark Noble ya taka shi.