Zaha ya bar Ingila ya koma Ivory Coast

Wilfried Zaha

Asalin hoton, FEDIVOIR.COM

Bayanan hoto,

Ingila ta yi asarar Zaha in ji Alan Pardew, kocinsa na Crystal Palace

Dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha ya zabi ya buga wa Ivory Coast wasa dag matsayinsa na dan wasan Ingila.

Zaha haifaffe Abidjan wanda ya girma Ingila, kuma ya buga wa Ingilan wasanni biyu ya koma buga wa kasarsa saboda wadanda ya buga wa Ingilan ba na wata gasa ba ne.

Dan wasan mai shekara 24, yan da damar buga gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2017 wadda za a yi a Gabon.

Gasar wadda za a fara ranar 14 ga watan JanairuJanuary, za ta iya sa Zaha ya rasa damar buga wa Palace wasannin sati shida.

Hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ta ce Zaha ya aika wa hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, takardun bukatar sauya kasar da yake yi wa wasa.