Nigeria ta kai wasan karshe a gasar kwallon mata

Super Falcons
Bayanan hoto,

'Yan wasan Najeriya za su yi kokarin sake komawa da kofin

Najeriya ta kai wasan karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka na 2016 na kwallon kafar mata da ake yi a Kamaru bayan ta fitar da Afrika ta Kudu da ci 1-0.

A ranar Asabar ne 3 ga watan Disamba Najeriyar mai rike da kofin za ta kara a wasan karshe da mai karbar bakuncin gasar Kamaru, wadda ta fitar da Ghana da ci 1-0 ita ma.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci ne 'yar wasan Najeriya Oparanozi ta ci wa Super Falcons kwallonta.

A ranar Asabar 3 ga watan Disambar nan ne za a yi wasan karshe a Yaounde, amma kuma za a yi wasan neman matsayi na uku ranar Juma'a, tsakanin Ghana da Afrika ta Kudu.