Gasar League Cup: Liverpool da Leeds

Jurgen Klopp

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Jurgen Klopp na fatan kai Liverpool wasan kusa da karshe na kofin EFL a karo na biyu

A ranar Talatar nan ne za a fafata a wasan db da na kusa da karshe na gasar cin kofin League Cup na Ingila tsakanin Liverpool da Leeds, da kuma Hull City da Newcastle.

Liverpool za ta yi wasan ba tare da Coutinho ba da Daniel Sturridge, yayin da Leeds wadda ke gasar kasa da Premier ta Championship, ba ta da matsalar masu rauni.

A tarihin haduwarsu hudu a gasar ta League Cup, Liverpool ta yi nasara sau biyu, sun yi canjaras sau daya.

Liverpool ta yi nasarar wuce wannan matakin na wasan dab da na kusa da karshe sau uku da taki shi.

Jurgen Klopp ya yi nasara a wasansa shida cikin takwas na League Cup a Liverpool.

Kocin dan Jamus na fatan kaiwa wasan kusa da karshe a karo na biyu.

Ba kungiyar da ta ci kwallaye a gasar a bana kamar Liverpool, inda ta ci kwallaye goma.

Leeds ta ki wannan mataki ne ne sau bakwai, inda ta yi nasar sau biyar.

Hull City da Newcastle:

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kocin Hull Mike Phelan ya ce yana dokin haduwarsa da kungiyar Rafael Benitez, Newcastle

Kocin Hull City Mike Phelan ya dauki karawar da muhimmanci sosai duk da yadda suke cikin hadrin faduwa daga Premier.

Kocin Newcastle Rafael Benitez ya ce, haduwarsu da kungiyar ta Premier abu ne mai karfafa guiwa.

Sau daya kungiyoyin biyu suka taba haduwa a gasar ta League Cup, kuma Newcastle ce a gidanta St James Park, ta yi nasara a zagaye na uku da ci 2-0 a kakar 1997-98.

A haduwa uku da Newcastle ta yi da Hull City, ba ta bari ta doke ta ba.

Hull za ta yi wannan kara wa ne a nasara uku da ta yi a gasar ta League Cup, bajintar da ba su taba yi ba a gasar.

Newcastle a tarihi ta ykai wasn dab da na kusa da karshe sau takwas, kuma guda daya kawai ta yi nasara.

A bana Newcastle ba ta bari an yi galaba a kanta ba a gasar a karawa uku, bajintar da duk wata kungiya ta taba yi kenan a gasar kawo yanzu.