'A hana masu shan abubuwan kara kuzari wasa har abada'

Usain Bolt

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Usain Bolt shi ne mutumin da ake ganin ya fi kowa gudu a duniya

Gwarzon dan tseren duniya na Jamaica Usain Bolt ya bayar da shawarar a rika haramta wa masu amfani da abubuwan kara kuzari shiga wasa har abada.

Dan tseren na Jamaica wanda ke rike da kambun gasar gudun mita 100 da 200 a duniya ya ce dalilin da ya sa ake ta ganin wannan matsala kusan a ko ina shi ne saboda hukumomi na kokari wajen gano masu laifin.

Dan tseren ya ce duk wanda aka kama ya yi amfani da abin da ke kara kuzari to kamata ya yi a hana shi wasa gaba daya, domin hakan ne ya fi kyau.

Sai dai ya ce akwai bukatar a yi la'akari da wadanda bisa kuskure ko wani sakarci za su samu kansu cikin matsalar, irin wadannan ya kamata a yi musu sassauci.

Bolt ya ce shawararsa ga matasan 'yan tsere da sauran wasanni ita ce, su kasance masu cike da kwarin guiwa da kwazo da himma.

Ya ce shi ma abin da ya yi kenan, ''ina alfahari, ina ba da himma ga duk abin da nake son zama.''