Kwallon Mata: Kamaru ta kai wasan karshe

'Yan wasan Kamaru
Bayanan hoto,

Kamaru na harin daukar kofin na kasashen Afirka na kwallon kafar mata a karon farko

Kamaru ta kai wasan karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka na 2016 na kwallon kafar mata da ta ke karbar bakunci bayan ta doke Ghana da ci 1-0.

A minti na 71 ne 'yar wasan Kamaru Raissa ta ci kwallon da ta ba su damar zuwa wasan na karshe a karawar da aka yi a Yaounde.

Yanzu za su jira wasan Najeriya mai rike da kofi, da Afirka ta Kudu da za a yi a garin Limbe nan da dan lokaci bayan kammala nasu, kafin su san da kasar da za su hadu da ita.

Wannan nasara ta sa har yanzu Kamaru na ci gaba da cin wasanninta, kuma ba a jefa mata kwallo ko da daya ba a raga.

A ranar Asabar 3 ga watan Disambar nan ne za a yi wasan karshe a Yaounde, amma kuma za a yi wasan neman matsayi na uku ranar Juma'a biyu ga watan na Disamba.