Kofin League: Liverpool da Hull City sun kai wasan kusa da karshe

Asalin hoton, Getty Images
Ben Woodburn wanda ya ci kwallo ta biyu, ya cancanci yi wa Ingila da Wales wasa
Liverpool ta kai wasan kusa da karshe na gasar kofin League Cup karo na uku a jere bayan da ta doke Leeds United da ci 2-0 a Anfield.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Divock Origi ya fara ci wa Liverpool din kwallonta a minti na 76.
Daga nan ne kuma sai matashi Ben Woodburn ya ci ta biyu a minti na 81.
Kwallon tasa ta sa ya kasance dan wasa mafi yarinta da ya ci wa Liverpool kwallo, yana da shekara 17 da kwana 45, kenan ya maye gurbin Micheal Owen.
Yanzu Liverpool za ta san kungiyar da za ta kara da ita a wasan kusa da karshe idan aka shirya jadawlin ranar Laraba.
Newcastle da Hull City:
Hull City ta doke jagora a gasar Championship ta kasa da Premier, ta 'yan dagaji Newcastle da ci 3-1 a bugun fanareti ta kai wasan kusa da karshe.
An yi bugun fanaetin ne bayan kammala minti casa'in ba ci, daga nan ne a Newcastle ta ci kwallo daya a cikin lokacin fitar da gwani, ta hannun Mohamed Diame, inda ya ci tsohuwar kungiyar tasa.
Bayan minti daya kacal sai Robert Snodgrass ya farke wa Hull City, wadda ta yi wasan lokacin fitar da gwanin gaba daya da 'yan wasa goma bayan da alkalin wasa ya kori Dieumerci Mbokani a minti na 89 sabod ya gwara wa Jamaal Lascelles kai.
A ranar Laraba ne kuma za a yi sauran wasanni biyu na neman wadanda za su kai wasan kusa da karshen, inda Arsenal za ta kara da Southampton, Manchester United za ta fafata da West Ham United.
Ga wasannin cin kofin Copa del Rey na Spaniya na ranar Laraba:
Toledo da Villarreal
Formentera da Sevilla
Real Madrid da Cultural Leonesa
Guijuelo da Atlético Madrid
Granada da Osasuna
Hércules da Barcelona
UCAM Murcia da Celta de Vigo