Derek Bell ya kusa kashe tsohon kocin Newcastle

Derek Bell

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Bell ya ce tunanin luwadin da tsohon kocin ya rika yi da shi, ya sa sau uku ya yi yunkurin hallaka kansa.

Tsohon dan wasan Newcastle Derek Bell ya ce ya yi niyyar kashe kocin da ya rika yi masa luwadi a shekarun 1970, George Ormond.

Koci George Ormond shi ne ya horar da Bell wasan kwallon kafa lokacin yana tsakanin shekara 12 da 16 yayin da yake wasa a kungiyar Montagu da kuma ta yara ta North Fenham.

A shekara ta 2002 aka yanke wa Ormond hukuncin zaman gidan yari na shekara shida bayan da aka same shi da tarin laifukan luwadi da kananan yara maza

Bell ya ce ya je gidan Ormond a karshe-karshen shekaraun 1990 da wata sharbebiyar wuka mai tsawon kamu guda, amma ya iske tsohon kocin ba ya nan.

Ormond ya shiga aikin kocin matasa a Newcastle United a wannan lokacin kafin daga baya ya bar kungiyar a watan Oktoba na 1998.

Bell ya ce ya kuduri aniyar tsophon kocin ne saboda tunanin yadda ya rika cin zarafinsa ta lalata, ya rika damunsa kusan a kodayaushe.

Tsohon dan wasan wanda ya buga wa Newcastle a farkon shekarun 1980, ya ce Ormond ya gana masa azaba ta luwadin sau daruruwan lokaci.

Bell ya ce ya sake zuwa gidan Ormond a wannan karon da rediyon dukar magana, wadda ya boye, domin ya nadi maganarsa yadda zai tona masa asiri.

Ya ce ya yi w tsohon kocin nasu tmbayoyi kan abin da ya sa ya yi masa wannan abu yana matashi, tare da yi masa barazana kan kada ya fada, da ba shi toshiyar baki sannan kuma da zama aminin gidansu bisa yaudara, amma Ormond ya ce bai san dalili ba, kuma ko sau daya bai ce yi hakuri ba.