An ba wa Southgate kocin Ingila na dindindin

Gareth Southgate
Bayanan hoto,

Tsohon dan wasan baya, Southgate, wanda ya yi wa Ingila wasanni 57, ya zama kocinta na dindindin na hudu a tsawon shekaru

An tabbatar wa Gareth Southgate aikin kocin tawagar kwallon kafar Ingila na dindindin a ranar Laraba, a lokacin taron hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA.

Tsohon kocin Middlesbrough Southgate, mai shekara 46 ya kulla yarjejeniyar shekara hudu, wadda za a rinka biyansa albashin kusan fan miliyan biyu a shekara.

Kafin ya shiga aikin horad da tawagar Ingila bai taba yin wani aiki na koci b, sai n shekar uku da ya yi da Middlesbrough, wadda ta fadi daga gasar Premier a karkashinsa a 2009.

A makon da ya wuce ne wani kwamiti na mutum biyar ya tantance Southgate, tsohon kocin twagar kasar ta 'yan kasa da shekara 21, wanda ya jagoranci Ingila wasanni hudu a matsayin kocin rikon kwarya, bayan saukar Sam Alladyce.

Ingila ta yi nasara a wasanni biyu na neman zuwa gasar kofin duniya, inda ta ci Malta 2-0, sannan ta doke Scotland 3-0, kuma ta yi canjaras 0-0 da Slovenia, ta tashi 2-2 da Spain a lokacin aikinsa na riko.

Taron hukumar kwallon kafar Ingilan na ranar Larabar zai kuma mayar da hankali kan tattauna batun zargin lalata da matasan 'yan wasa, domin ganin yadda za a kare aukuwar hakan a gaba.