Dan boksin na sume kwana 12 bayan doke shi

Eduard Gutknecht

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Gutknecht ya jure har karshen damben da Groves duk da raunin da aka yi masa a turmi na 10

Dan damben boksin na Jamus Eduard Gutknecht har yanzu yana can a sume kwanaki 12 bayan karonsa da George Groves, na Burtanita.

Abokin damben nasa ne dai ya bayar da wannan sanarwa, cewa Gutknecht, wanda ke bukatar a yi masa tiyata bayan fadan, b ya cikin yanayi mai tayar d hnkali, kamar yadda hukumar damben boksin ta Burtaniya ta bayyana.

Dan damben mai shekara 34 ya kamu da ciwo ne a dakin sauya kayansa jim kadan bayan kammala damben nasu, wanda aka yi nasra a kansa a ranar 18 ga watan Nuwamba, inda aka garzaya da shi asibiti.

Groves, wanda ya doke Bajamushen ya cigaba da rike kambunsa na matsakaita nauyi na hukumar dambe ta duniya ta WBA.

Yanzu ya kafa wani asusu na tara kudin da za a taimaka wa abokin damben nasa da iyalansa.