An haramta wa Mourinho wasa daya

Jose Mourinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mourinho ya amince da laifin rashin da'a

An haramta wa Jose Mourinho kasancewa tare da yan wasansa a fili na tsawon wasa daya kan laifin nuna rashin da'a lokacin wasansu da West Ham ranar Lahadi wanda suka tashi kunnen doki 1-1.

An yi wa kocin na Manchester United wannan hukuncin ne tare da cin tararsa fan 16,000, bayan da alkalin wasa ya kore shi daga cikin fili zuwa wurin 'yan kallo a wasan na Premier.

Wannan na nufin kocin ba zai kasance da 'yan wasansa ba a karawarsu ta daren Laraba da West Ham ta wasan dab da na kusa da karshe na kofin League Cup a Old Trafford.

Alkalin wasa Jon Moss ya kori Mourinho ne bayan da ya yi bal da robar ruwa a fusatar da ya yi saboda alkalin wasan ya ba wa Paul Pogba katin gargadi saboda ya fadi kamar kyaftin din West Ham Mark Noble, ya taka shi.

Kocin mai shekara 53 ya amsa laifinsa da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi masa na nuna rashin da'a.

Sai dai hukuncin bai hana shi gana wa d 'yn wasn nasa ba kafin fara karawar ta Laraba da lokacin hutun rabin lokaci da kuma bayan wasan, sanna yana iya sadarwa da su daga cikin kallo da yake.

Wnna shi ne karo na biyu da ake tuhumar kocin dan Portugal a cikin wata biyu, inda aka kore shi a wasansu da Burnley na ranar 29 ga watan Oktoba.

Daga baya aka hana shi halartar wasa daya, aka kuma ci shi tararsa fan dubu takwas.