Kofin League: Southampton ta yi waje da Arsenal

Jordy Clasie Scores his first goal for Southampton

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jordy Clasie ya ci wa Southampton kwallonsa ta farko

Southhampton ta kai wasan kusa da karshe gasar cin kofin League Cup na Ingila bayan ta doke Arsenal 2-0 a Emirates

Clasie ne ya ci wa bakin kwallonsu ta farko a cikin minti na 13 da shiga fili, kafin Bertrand kuma ya ci ta biyu can aminti na 38.

A karawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar Premier, ranar 10 ga watan Satumba, Arsenl ce ta ci Southampton 2-1 a Emirates.

A tarihi a wasanni uku da Arsenal ta yi na gasar ta League Cup da wata kungiyar Premier a gidanta ta yi rashin nasara ne.

Sai dai kuma a haduwar Arsenal din da Southampton sau bakwai a League Cup sau daya Arsenal ta yi rashin nasara.

Amma kuma a wasannin da Arsenal ta yi na wasan dab da na kusa da karshe na Leagu Cup guda biyar sau daya ne kawi ta wuce matakin, inda a 2010-11 ta ci Wigan 2-0.

Tun a ranar Talata Liverpool da Hull City suka yi nasarar zuwa wasan kusa da karshe na gasar.

Jadawalin wasan kusa da karshe:

Manchester United za ta kara Hull City, yayin da Southampton za ta fafata da Liverpool.

Za a yi karon farko a makon cikin sati na biyu na watan Janairu da zai fara ranar tara ga watan na Janairu, sannan a yi karo na biyu a makon da zai fara 23 ga watan Janairu.