League Cup: Man United ta kai wasan kusa da karshe

Martial Scoring against West Ham

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Kwallo hudu kenan Martial ya ci wa Man United a bana

Manchester United ta yi nasarar zuwa matakin wasan kusa da karshe na gasar cin kofin League Cup bayan ta casa West Ham a Old Trafford da ci 4-1.

An yi wasan ne ba tare da kocin United ba Jose Mourinho wanda yake can kan benen 'yan kallo, saboda haramta masa zuwa cikin filin da aka yi.

Hukumar FA ta same shi ne da laifin rashin da'a a wasansu na ranar Lahadi da West Ham din, lokacin da ya yi bal da robar ruwa don an ba wa Paul Pogba katin gargadi.

Manchester United ta yi nasarar zuwa wasan kusa da karshe a gasar ta League Cup a karon farko tun kakar wasa ta 2013-14.

Zlatan Ibrahimovic ne ya fara ci wa United kwallonta a cikin minti biyu da wasa, kafin tsohon matashin dan wasan United din Ashley Fletcher ya rama a minti na 35.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne sai Martial ya ci wa Manchester United kwallonta ta biyu a minti na 48, sannan kuma a minti na 62 ya sake daga raga

Ana dab da tashi ne kuma bayan cikar mintina 90 na wasan sai Zlatan Ibrahimovic ya sake cin bakin kwallo ta hudu.

Jadawalin wasan kusa da karshe:

Manchester United za ta kara Hull City, yayin da Southampton za ta fafata da Liverpool.

Za a yi karon farko a makon cikin sati na biyu na watan Janairu da zai fara ranar tara ga watan na Janairu, sannan a yi karo na biyu a makon da zai fara 23 ga watan Janairu