Blatter zai ji sakamakon karar da ya daukaka

Fifa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Blatter ya fara jan ragamar Fifa daga tsakanin 1998 zuwa 2015

A ranar Litinin kotun daukaka kara ta wasanni ta duniya za ta yanke hukunci a kan karar da tsohon shugaban FIFA, Sepp Blatter, ya daukaka a gabanta.

Sepp Blatter ya daukaka karar ne yana neman a yi watsi da hukuncin da kwamitin da'a na hukumar FIFA ya zartar, wanda ya hana shi shiga sabgogin tamaula har tsawon shekara shida.

Tun farko kwamitin na da'a ya haramta wa Blatter da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini, shiga harkokin wasanni har tsawon shekara takwas, daga baya kwamitin daukaka kara na FIFA ya rage hukuncin zuwa shekara shida.

An samu tsofaffin shugabannin na FIFA da laifin karya ka'idar aiki, inda aka biya Platini ladan aiki na kudi fam miliyan daya da dubu dari uku.

Dukkansu sun musanta aikata ba daidai ba a lokacin da suka gudanar da aikinsu a FIFA.