Iniesta zai warke daga rauni kafin El Clasico

La Liga

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Real Madrid ce ke kan teburin La Liga a matsayi na daya

Watakila kyaftin din Barcelona, Andres Iniesta, ya murmure daga raunin da ya yi, ya kuma fara wasa a karawar da kungiyar za ta yi da Real Madrid a ranar Asabar.

Iniesta mai shekara 32, bai buga wa Barcelona wasanni bakwai ba, sakamakon jinya da yake yi, kuma daga cikinsu wasanni uku kungiyar ta ci.

Barcelona mai rike da kofin La Liga tana mataki na biyu a kan teburi, inda Real Madrid, wadda ke matsayi na daya, ta ba ta tazarar maki shida.

Shi kuwa dan wasan Real Madrid, Gareth Bale, ba zai buga wasan El Clasico ba saboda raunin da ya yi, wanda ake cewa zai dauki watanni da dama kafin ya warke.

Sai dai kuma Toni Kross na Real Madrid ya yi atisaye a ranar Juma'a tare da sauran 'yan wasan kungiyar, bayan da kungiyar ta yi wasanni hudu ba shi.