El Clasico: Barcelona da Real Madrid

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ce za ta ziyarci Barcelona a Camp Nou

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 14 na gasar La Liga--karon battar da ake yi wa lakabi da El Clasico.

Bayan da aka buga wasannin mako na 13 a gasar cin kofin La Liga ta bana, Real Madrid ce ke kan gaba a teburi da maki 33, yayin da Barcelona ke biye da ita da maki 27.

A cikin karawa 13 da kungiyoyin biyu suka yi a baya a gasar ta La Liga, a wasanni uku ne Barcelona ta yi rashin nasara.

Real Madrid ta ci Barcelona a karawa biyar a wasanni tara da suka yi gumurzu a gasa dabam-dabam.

Lionel Messi na Barcelona shi ne dan kwallon da ya fi cin kwallo a karawar ta El Clasico inda ya ci 21, daga ciki ya ci hudu a wasanni biyar da suka kara.