Wa zai yi nasara tsakanin Man City da Chelsea?

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ce za ta ziyarci Ettihad

Manchester City za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar cin kofin Premier wasan mako na 14 a ranar Asabar.

Wannan shi ne karo na 154 da kungiyoyin biyu za su kece raini a tarihi, inda City ta ci wasanni 52, Chelsea ta samu nasara a wasanni 62 suka yi canjaras sau 39.

A gasar cin kofin Premier ta bara, City ce da doke Chelsea 3-0 a Ettihad, sannan ta kara doke ta 3-0 a Stamford Bridge, yayin da Chelsea ta samu nasara a kan City da ci 5-1 a gasar FA.

Chelsea ce ke mataki na daya a kan teburin gasar Premier da maki 31, yayin da Manchester City ke matsayi na uku da maki 30.