Luwadi: Wani tsohon dan Newcastle shi ma ya magantu

Asalin hoton, DAVID EATOCK
David Eatock ya ce tsawon shekara uku Geroge Ormond ya rene shi, yana kuma cin zarafinsa
Tsohon dan wasan Newcastle David Eatock ya zama na baya-bayan nan da ya fito fili ya bayyana cewa kocinsu George Ormond ya ci zarafinsa da luwadi yana matashi.
Eatock ya sheda wa BBC cewa Ormond wanda aka daure shekara shida daga baya, shi ne ya rene shi a wasan kwallon kafa, lokacin yana tsakanin shekara 18 da 21.
Eatock, wanda yanzu ya kai shekara 40, ba ya daga cikin mutum bakwai, wadanda suka shigar da karar cin zarafin da aka daure Ormond a 2002 a kanta, amma kuma yanzu ya gabatar wa 'yan sanda kokensa.

Asalin hoton, David Eatock
Eatock ya ce ya lalace a lokacin da ya bar kungiyar, idan ya duba yadda yake a da
Ya fito da zargin nasa ne a yayin da kungiyar da ke kare mutuncin yara daga lalata ta Burtaniya (NSPCC), ta ce ya zuwa yanzu ta sami korafi 860 a cikin mako daya da kafa ta.
Sabon kocin Ingila Gareth Southgate, wanda yawancin wadanda ke zargin an yi musu luwadin, sa'o'in wasansa ne, ya ce, ''lamarin abin takaici ne.''