Kane ya yi sabon kwantiragi daTottenham

Asalin hoton, AFP
Harry Kane wanda Tottenham ta rene shi ya fara yi mata wasan Premier a 2014
Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane ya sabunta kwantiraginsa da Tottenham inda zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa shekara ta 2022.
Yarjejeniyar ta yanzu ta tanadi ba shi albashin sama da fan dubu 100 a sati, kuma ta maye wadda ya kulla da kungiyar ta shekara biyar a baya wadda ya sanya wa hannu a Fabrairun 2015.
Da yake sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar Kane mai shekara 23, wanda ya ci wa Ingila kwallo biyar a wasanni 17 ya ce, ''kowa ya san yadda nake kaunar kungiyar nan.
Asalin hoton, Harry kane
Harry Kane na rattaba hannu a sabon kwantiragi
''Saboda haka kulla sabuwar yarjejeniya da ita wata kauna ce ta musamman, muna da matasan 'yan wasa masu kokari, kuma kungiyar na tafiya daidai.''
A bana Kane ya ci wa Tottenhma kwallo shida a wasanni goma da ya yi mata, duk da cewa bai samu damar buga wasanni 10 ba saboda raunin da ya ji a kafa.
Dan wasan ya ci kwallo 21 a manyan wasanni na 2014-15 kuma ya samu kyatar takalmin zinare (Golden Boot), a matsayin wanda ya fi cin kwallo, inda yake da 25 a Premier ta bara.